Ana ci gaba da cece-kuce kan email din Clinton

Misis Clinton. Hakkin mallakar hoto
Image caption Kawuna dai sun kara daukar dumi, a daidai lokacin da baban zabe ke karatowa a Amurka.

Wani alkali a Amurka yace dole ne 'yar takarar shugaban kasa ta jam'iyyar Democrats Hillary Clinton ta bada amsa a rubuce kan yadda ta yi amfani da adireshin Email na kashin kan ta a lokacin da ta ke sakatariyar harkokin wajen kasar.

Wata kungiyar masu ra'ayin mazan jiya ta Juducial Watch, ita ce ta gurfanar da Misis Clinton a gaban kuliya manta sabo, tare da bukatar ta kare kan ta.

Karkashin tsarin shari'ar Amurka, Hillary Clinton ta na da kwanaki talatin nan gaba da za ta bada amsa a rubuce kan tambayoyin da kungiyar ta yi mata.

A baya dai Misis Clinton ta nemi afuwa kan amfani da mail na kashin kan a lokacin da take bakin aiki.

A watan da ya gabata ne dai hukumar FBI ta yi watsi da binciken da ake yi kan wanna batu, ba tare da tuhume ta da aikata ba daidai ba.