Jamus na shirin hana mata sanya burƙa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu kasashen yamma kamar Faransa tuni suka hana musumai sanya burka

Ministan harkokin cikin gida na Jamus, Thomas de Maiziere, ya yi kira da a hana mata sanya burƙa da ke rufe fuska ruf a ƙasar.

Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan ya ce kafa dokar hana sanya burƙa kwata-kwata ba zai zo daidai da tsarin mulkin ƙasar ba.

Mista De Maiziere ya shaida wa wani gidan talbijin na ƙasar cewa, a hukunce gwamnati na so mata su buɗe fuskarsu a wuraren da ya zama dole saboda hakkin jama'a.

Tsarin wanda zai buƙaci amincewar majalisar dokokin ƙasar zai hana rufe fuska a makarantu da jami'o'i da wuraren renon yara da ofisoshin gwamnati da kuma a yayin tuƙa abin hawa.

Cece-kuce kan haramta rufe fuskar ta janyo rabuwar kawuna a gwamnatin hadin-gwiwa ta Angela Merkel mai mulkin ƙasar.

Labarai masu alaka