'Tafasa muke ci mu da 'ya'yanmu'

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Alƙaluma na baya-bayan nan da ƙungiyar likitoci ta Medecin sans frontiere ta fitar, sun nuna cewa mutanen da ke matuƙar buƙatar agajin gaggawa a Najeriya sun haura 500,000.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar da ke arewa-maso-gabashin Najeriya da BBC ta zanta da su sun ce suna yin bara kuma suna shiga daji domin yin tafasa.

An jima ana zargin cewa wasu batagari na sauya akalar abincin da ya kamata a kai wa 'yan gudun hijirar.

Gwamnati ta ce ta fara bincike a kan lamarin.

Hakkin mallakar hoto NEMA
Image caption Gwamnatin Najeriya ta ba da izinin kai wa 'yan gudun hijira shinkafa, amma ba san inda suke ba

Labarai masu alaka