Haiti: MDD ta yi amai ta lashe

'Yan Haiti na karbar maganin cutar Cholera Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Majalisar dai ta ki amincewa da aikata ba daidai ba.

Bincike daban-daban da masana kimiyya suka yi sun nuna cewa dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya daga Nepal su ne sanadin barkewar annobar kwalara a Haiti, annobar da ta kashe mutum 10,000.

Amma, haka aka kwashe shekara biyar Majalisar Dinkin Muniyar na musanta cewa ita ce da alhakin barkewar annobar, saboda a cewarta abu ne mawuyaci a tabbatar da zargin.

Sai dai yanzu majalisar dinkin duniyar ta sauya wannan matsayin. Mai magana da yawun babban sakataren majalisar Ban Ki Moon ya fito ya amice cewa da rawar da majalisar dinkin duniya ta taka a farko-farkon barkewar annobar, yana karawa da cewa abubuwan da suka faru a tsawon shekara guda da ta wuce na nuna cewa akwai bukatar a tsaya sosai a kan lamarin.

Majlisar Dinkin Duniyar dai ta sauya matsayin ne bayan fitar wani rahotonta na sirri da aka tsegunta wa jaridar New York Times, wanda ya nuna cewa ba don wasu ayyuka da majalisar ta yi ba, da annobar kwalarar ba ta barke ba.

Sai dai duk da wannan rahoton, ba ta sauya matsayinta ta fuskar shara'a ba. Wasu kotuna a Amurka sun yi watsi da bukatar biyan diyya da wasu iyalai suka nema, suna cewa majalisar dinkin duniya na da kariya, ba dama a gurfanar da ita gaban kuliya.

Labarai masu alaka