Ana daukar yara yaki a Sudan ta Kudu -UNICEF

Hakkin mallakar hoto AFP

Asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya ce ana ɗaukar yara masu yawa domin su yi yaƙi a Sudan ta Kudu.

Mataimakin shugaban asusun, Justin Forsyth, ya shaida wa BBC cewa yara 600 ne aka yi amfani da su wajen yaƙi tun daga farkon wannan shekarar.

Inda ya ƙara da cewa magoya bayan mataimakin shugaban ƙasar, Riek Machar da kuma shugaba Salva Kiir sun kara kaimi wajen ɗaukar yara tun lokacin da sabon rikici ya ɓarke a watan Yuli.

Mista Forsyth ya ce matsalar tamowa ta ya yaɗu kuma ana fuskantar barazanar yunwa a wasu yankunan.

Labarai masu alaka