'Al'umomin kusa da Madatsun ruwa na wahala'

A Najeriya, gwamnonin jihohin da ke samar da wutar lantarki daga madatsun ruwa sun ce al'umominsu da ke zagaye da madatsun na cikin wani mawuyacin hali sakamakon aikace-aikacen madatsun.

A karshen wani taro da suka yi a ranar Alhamis, gwamnonin jihohin biyar sun ce al'umomin na fuskantar matsalolin lalacewar muhalli, da ambaliyar ruwa, kuma bugu da ƙari ga rashin samun wutar lantarki.

Hakan a cewarsu ya faru ne saboda gazawar gwamnatin tarayyar wajen kafa wata hukuma da za ta riƙa kula da madatsun ruwan.

Sai dai gwamnatin tarayyar ta ce za ta yi iya ƙokarinta wajen tabbatar da hukumar ta soma aiki.

Labarai masu alaka