Afghanistan: An kwato Kunduz daga hannun Taliban

Hakkin mallakar hoto EPA

Dakarun gwamnatin Afghanistan sun sake kwato lardin Kunduz mai matukar muhimmanci daga hannun mayakan Taliban.

Gwamnan lardin Asadullah Omarkhel ne ya sanar da haka, sa'oi bayan da mayakan na Taliban suka kwace gundumar Khanabad.

Amma wasu majiyoyi a yankin sun ce har yanzu mayakan Taliban din na nan a kusa da helkwatar gundumar.

Dakarun gwamnatin na kokarin ganin sun sake bude hanyar da ke hadewa da birnin Kunduz.

Wata kafar talabijin mai zaman kanta a Afghanistan ta bada rahoton cewa, dakarun gwamnati sun sake kwato gundumar ta Khanabad, dake da tazarar kilomita 30 (mil19) daga gabashin Kunduz.

Mayakan Taliban din sun yi ta kai farmaki daga kusurwa daban-daban, da hakan ya tilasta wa dakarun gwamnati ja da baya zuwa birnin Kunduz, da ya koma hannun Taliban din a bara.

Labarai masu alaka