Nigeria: 'Za mu hukunta dan danfarar alhazai'

Ka'aba Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Maniyyan dai ba za su samu damar zuwa aikin hajjin bana ba.

A Najeriya, Gwamnan jihar Nasarawa, Umaru Tanko Almakura ya ba da umurnin a nemo wani jami'in hukumar Alhazan jihar da ya damfari wasu maniyyata domin a hukunta shi.

Gwamnan ya bayyana damfarar da cewa rashin imani ne a ce an cuci mutanen da suka hada taro da sisi suka biya kudin kujera su je sauke farali.

Sai dai Almakura ya ce a halin da ake ciki gwamnati ba za ta dauki dukiyar jihar ta biya mutanen da aka damfara ba, amma za ta yi bakin kokarin ta dan ganin an damko mutumin.

Za kuma a gurfanar da shi gaban hukuma, matukar aka same shi da laifi kuma dole ya biya mutanen hakkin su.

Kimanin maniyyata hajjin bana talatin ne jami'in ya damfara, kana ya gudu, kuma har yanzu ba a ji duriyarsa ba.

Labarai masu alaka