Angola: An sake zaben shugaba Eduardo dos Santos

A sake zaben shugaban kasar Angola Jose Eduardo dos Santos, a matsayin shugaban jam'iyar MPLA mai mulkin kasar a zaben da aka gudanar.

Mai shekaru 73, Mr Santos ya shafe shekaru 36 yana mulkin kasar.

A shekara mai zuwa ne ake sa ran gudaar da zaben majalisar dokoki, kuma ko tantama babu shugaban jam'iya mai mulki shine zai zama shugaban kasa.

A baya dai cikin wannan shekarar Mr dos Santos ya ce zai sauka daga mulki a shekara ta 2018, amma kuma ya sha yin irin wannan alkawari a baya.

An sha sukar sa kan danka harkokin mulki da arzikin kasar ga 'yanuwansa da kuma aminansa na siyasa.

Labarai masu alaka