Rio:Brazil ta ci zinare a bugun fenareti

Hakkin mallakar hoto Getty

Tawagar kwallon kafa ta maza ta kasar Brazil ta ci zinare karo na farko a gasar Olympics, bayan ta doke Jamus da ci 5-4 a bugun Fenareti.

Golan Brazil Weverton ne ya kade bugun karshe da Jamus ta yi, yayin da Neymar jefa kwallon karshe a ragar Jamus.

Dukkan bangarori biyun dai sun yi rabuwar kare-jini biri-jini ne a karawar minti casa'in da suka yi, inda suka tashi 1-1, kuma daga nan ne aka yi karin lokaci.

Da wannan nasarar, Brazil ta lashe zinare, Jamus ta samu azurfa, Najeriya kuma ta kasance ta uku ta samu tagullu bayan ta lallasa Honduras da ci 3-2 a Belo Horizonte

Labarai masu alaka