An bude sabuwar gadar gilashi a kasar China

Kasar China ta kaddamar da bude gadar da aka yi da gilashi a hukumance, don amfanin masu yawon bude ido.

Gadar wacce wasu karafuna ne ke rike da ita na lilo ne, kana hanyarta na danganawa tsakanin dogayen tsaunuka biyu.

Tana da tsawon mita dari tara da tamanin (980) , tana kuma nesa da kasan birnin Zhangjiajie a gundumar Hunan da mitoci dari uku ( 300) daga , kusan kamar ace tsawon gidan bene mai hawa ashirin (20).

Masu ziyara na iya kallon kasan ta cikin gilashin da ke da kaurin fiye da kashi ashirin da biyar bisa dari ( 21%) na sauran gilasai.

Gadar na da ingancin da mota za ta iya bi, amma an yi ta ne kawai saboda masu tafiyar kafa -- akalla mutane dubu takwas a ko wace rana.

Gadar gilashi da kuma hanyoyin cikin tsaunuka sun zama wani abin yayi a kasar ta China, inda ake zuwa yawon shakawata ana daukar hotuna musamman ma na bukukuwan aure.

Labarai masu alaka