Ku guji tsaurin addini — Sarkin Morocco

Sarki Muhammad na Morocco Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sarki Muhammad ya umarci 'yan kasar su rungumi zaman lafiya a duk inda suke.

Sarki Muhammad na 6 a Morocco, ya yi kira ga 'yan kasar da ke zaune a kasashen waje, yawancin su nahiyar turai su rungumi tsarin addinin musulunci mai sassauci, su kuma guji masu kaifin kishin islama.

Wanna shi ne karo na farko da sarki Muhammad ya yi kira ga al'umar kasar a duk inda suke a fadin duniya, a wani mataki na wayar da kan su bayan hare-hare na baya-bayan nan da masu kaifin kishin islama suka kai a kassahen turai.

Hare-haren dai sun rutsa da wasu daga cikin 'yan Morocco mazauna kasashen turai, ya kuma yi allawadai kan kisan wadanda ba su san hawa ba bare sauka, ya kuma kira kisan da aka yi wa wani malamin addinin kirista a Faransa da abun da ba za a taba yafewa maharin ba.

Sarki Muhammad ya kara da cewa, kaifin kishin islama zai bata matasa, su yada abinda sam ba koyarwar islama ba, da kuma janyo masa bacin suna.

Labarai masu alaka