Nigeria ta tsira da tagulla a Rio

Hakkin mallakar hoto Getty

Najeriya ta lashe lambar yabo ta tagulla a gasar wasanni ta Rio, bayan da kungiyar kwallon kafa ta kasar ta maza ta lallasa Honduras da ci 3-2 a Belo Horizonte.

Sadiq Umar ne ya ci wa Najeriya kwallaye biyu, yayin da Aminu Umar ya zura ta uku.

Wannan ce lambar yabo ta uku jumulla da Najeriya ta samu a fagen kwallon kafa a wasannin Olympics daban daban.

Najeriya ce ta lashe lambar yabo ta zinare a wasan kwallon kafa na gasar Olympics ta Atlanta a 1996, inda ta doke Argentina da ci 3-2.

Sai dai a 2008, Argentina ta rama inda ta doke Najeriyar a wasan karshe, abin da yasa Najeriyar ta tsira da lambar yabo ta azurfa.