An kai hari gidan biki a Turkiyya

Harin da aka kai gidan biki a Turkiyya. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jihar Gaziantep ta sha fuskantar hare-haren 'yan IS.

Jami'ai a Turkiyya sun ce akalla mutane 30 ne suka rasu wasu 90 suka ji mummunan rauni, a lokacin da wani bam ya tashi a wurin bikin aure a jihar Gaziantep da ke kudu masu gabashin kasar.

Mataimakin firaiministan kasar Mehmet Simsek, yace harin ya yi kama da na kunar bakin wake.

Manyan motocin daukar marasa lafiya ne suka cika wurin da aka kai harin wanda ya ke tsakiyar jihar.

Shi ma gwamnan Gaziantep Ali Yerlikaya ya bayyana harin da na ta'adda, ya yin da dan majalisa Samil Tayar, ya wallafa a shafin sa na twitter cewa mayakan kungiyar IS ne suka kai harin.

Wakilin BBC yace kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, amma majiyar gwamnati na cewa ana nuna yatsa kan kungiyar IS.

A baya dai jihar Gaziantep mai iyaka da kasar Syria ta sha fuskantar hare-haren 'yan kungiyar.

Labarai masu alaka