Yemen:An jefa bama-bamai kusa da masu zanga-zanga

An bada rahoton jefa wasu bama-bamai ta sama kusa da dandazon masu zanga-zanga a Sanaa babban birnin kasar Yemen

Daruruwan mutane ne ke zanga-zangar nuna adawa da hare-hare ta saman da dakarun kawancen da kasar Saudia ke jagoranta ke kai wa.

Babu dai wasu rahotannin da suka bayyana samun jikkata

Hadakar na mara wa gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita baya kan 'yan tawaye.

Amma kuma kasar Saudia na fuskantar suka a kai a kai daga kungiyoyi masu rajin kare hakkin biladama, kan yadda ake hallaka da kuma jikkata fararen hula a hare-haren.

Rundunar sojin Amurka ta ce ta rage adadin yawan jami'an tsaronta masu bada shawara dake tallafawa farmakin da dakarun kawancen ke kai wa.