Ana zanga-zanga a Yemen

Masu zanga-zanga a Yemen
Image caption Masu boren na goyon bayan sabuwar gwamnatin kasar ta kabilar Houthi.

Dubban mutane ne suka fito dan yin zanga-zanga a babban birnin kasar Yemen wato Sanaa, su na dai nuna adawa da kawancen da Saudiyya ke jagoranta na kai hare-hare ta sama a kasar.

Harwayau masu boren na nun agoyon bayan sabuwar gwamnatin kasar da 'yan tawaye mabiya darikar shia suke jagoranta, wadanda suka hambarar da gwamnatin da kasashen yammacin duniya ke marawa baya, kana su ka karbe iko da birin tun shekarar da ta wuce.

Kawancen da ke yaki da 'yan tawaye na kabilar Houthi na kai hare-hare ta sama da kasa a tsaunukan kasar ke da kallon fadar shugaban Yemen.

Ganau kan lamarin sun shaidawa BBC cewa yawancin masu boren sun arce cikin tashin hankali saboda luguden wutar da ake musu.

gwamnatin Saudiyya dai na shan suka daga kungiyoyin kare hakkin bil'adam da kassahen duniya kan kashe fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba da ake yi a kasar ta Yemen.

Labarai masu alaka