Isra'ila ta kai hari Gaza

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Benjamin Netanyahu, Framistan Isra'ila

Dakarun Isra'ila sun ce, jiragensu na yaki da tankoki sun kai hari a garin Beit Hanoun a arewacin yankin Gaza.

Harin na maida martani ne ga harin roka da Falasdinawa masu fafitika suka kai.

Harin roka da Falasdinawa suka kai a garin Sderot bai haddasa rauni ba, ko wata ɓarna.

Harin Isra'ila na ranar Lahadi ya shafi wuraren da suke da alaƙa da ƙungiyar Hamas.

Rahotannin Falasdinawa na cewa, mutane hudu sun jikkata.

Labarai masu alaka