IS ce ta kai hari gidan biki — Erdogan

Harin da aka kai gidan biki a Turkiyya. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jihar Gaziantep ta sha fuskantar hare-haren 'yan IS.

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya ce yana kyautata zaton cewa kungiyar IS ce ta kai hari a wani gidan biki a Gaziantep, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutune da dama.

Jami'ai sun ce yanzu haka kididdigar wadanda suka mutu ta kai 50 sannan kuma wadanda suka jikkata sun kusa 100.

Wani dan kunar-bakin wake ne dai ya kutsa cikin manyan baki a dai-dai lokacin da suke yin rawa a kan titi, a daren ranar Asabar.

Daman dai dan majalisa Samil Tayar, ya wallafa a shafinsa na twitter cewa mayakan kungiyar IS ne suka kai harin.

Wakilin BBC yace kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin.

Garin na Gaziantep dai yana kan iyakar Syria kuma ya yi kaurin suna wajen kasancewa mafaka ga 'yan kungiyar ta IS masu dama.

A baya dai Gaziantep ya sha fuskantar hare-haren 'yan kungiyar.

Labarai masu alaka