Lukaku zai ci gaba a Everton — Koeman

Image caption Romeolu Lukaku, dan wasan gaba na Everton

Kocin Everton, Ronald Koeman ya ce dan wasan kulob din na gaba, Romelu Lukaku zai ci gaba da kasancewa a Everton har zuwa "akalla sabuwar kakar wasa ta nan gaba".

Rahotanni dai sun ce Lukaku mai shekara 23 ya yi yunkurin barin Everton.

An kuma ce kulob din Chelsea ne yake zawarcin dan wasan dan asalin kasar Belgium.

Koeman ya ce " Cigaba da zaman Lukaku, babban labari ne ga kowa."

Da kuma aka tambayi Koeman ko za a tsawaita kwantaragin zaman Lukaku a Everton, sai ya ce "Akwai yiwuwar."

Labarai masu alaka