Sakkwato: Ana zargin wasu da auren jinsi

Image caption sakkwato

'Yan sanda a Najeriya sun kama wani mutum da ake zargin cewa wasu maza sun daura auren jinsi guda a gidansa da ke Sakkwato a arewacin kasar.

Kakakin 'yan sanda a jihar ya shaida wa BBC cewa, suna ci gaba da neman mazan da ake zargi da yin auren.

Wata majiya ta bayyana cewa mutanen da ake zargi da yin auren sun fito ne daga wata jiha, inda aka hanasu daura auren, sai suka je Sakkwaton domin yin auren tsakanin namiji da namiji.

Dokokin Nigeria sun haramta auren jinsi guda.

Labarai masu alaka