'Likitoci na rubuta magani fiye da kima don kuɗi'

Image caption Masu binciken sun buƙaci a inganta yadda ake rubuta wa marasa lafiya magani a yankin

Wani binciken da aka yi ya nuna cewa likitoci a ƙasashen da ke kudu da Sahara na rubuta wa marasa lafiya magani fiye da kima saboda neman kuɗi.

Binciken na ƙasa da ƙada wanda jami'ar London da kuma wata cibiyar manufofi kan kiwon lafiya suka gudanar ya yi nazari a kan ƙasashe 11 da ke yankin.

Inda ya gano cewa ana rubutawa marasa lafiya magunguna a ƙalla kala uku idan sun je ganin likiti sau ɗaya, wanda hakan ya ɗara magunguna biyu a ƙa'idar hukumar lafiya ta duniya.

Binciken ya ce matsalar ta fi ƙamari a cibiyoyin lafiya na kuɗi.

Masu binciken dai sun yi gargaɗin cewa rubuta magani fiye da kima zai iya janyo kuskure da shan magani fiye da kima da kuma mummunan illa ga wanda ya sha.

Hakazalika an gano cewa ana bai wa marasa lafiya magungunan kashe ƙwayoyin cuta ba tare da an duba su sosai ba, abin da zai jefa su cikin haɗarin daukar cututtuka da kuma bijirewa magani.

Labarai masu alaka