Ambaliyar ruwa ta kashe mutane a India

A India dubban mutane sun kauracewa gidajen su sakamakon cika makil da wasu kogin Ganges da wasu kogunan su ka yi, abinda kuma ya janyo ambaliyar ruwa.

Ruwan ya mamaye yankuna da dama a jihohin Bihar da Uttar Pradesh da yammacin Bengal da Madhya Pradesh da kuma Rajasthan, sannan fiye da mutane talatin sun mutu.

Mutane da dama sun makale a kan rufin gidaje, sannan sun ce ba su da isasshen abinci da ruwan sha.

An tura sojoji domin aikin ceto. An kuma kafa sansanonin taimako da yawa, amma wasu mutanen har yanzu na kwana a waje.

Kafofin sada zumunta na yi wa ministan yankin Medhaya Pradesh ba a, wanda aka dauki hoton sa 'yan sanda sun ciccibe shi a yankin da ruwan ya mamaye.

Wasu na kwatanta daukar da aka yi masa da cewa tsari ne na mulkin mallaka.

To sai dai wani jami'i ya kare shi, inda yace wajen na da santsi, kuma akwai yiwuwar saran macizai da kuma kunama a wajen.

Labarai masu alaka