Rasha ta dakatar da amfani da sansani jiragen saman Iran

Hakkin mallakar hoto Ilna

Rasha ta tabbatar cewa ta dakatar da amfani da sansanonin jiragen saman Iran wajen kai hare-hare a Siriya - akalla a halin yanzu.

Janyewar ta biyo bayan sukar da Ministan Tsaron Iran ya yi a kan shaida ma duniya da Rahsar ta cewa tana amfani da sansanin Iran din.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran din, Bahram Ghasemi, ya ce a halin yanzu an tsaida hare-haren da Rashar ke kaiwa daga sansanin.

Ya ce, "Da ma shiri na wucingadi, aiki na musamman, Rasha ba ta da sansani a Iran, ba a kuma sauke ta a wani sansani ba.

"Rashar ce ta nemi alfarmar wani shiri na dan lokaci, an kuma yi an gama a halin yanzu."

Kasashen Rasha da Iran dai na goyon bayan shugaba Bassharul Asad na Rasha ayakin da ake a Syria, sai dai Iran ba ta bayar da cikakken bayanai kan irin rawar da take takawa a rikicin.

Labarai masu alaka