Jam'iyyar adawa ta ƙwace Johannesburg

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jocob Zuma, shugaban Afirka ta kudu

Jam'iyyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudu ta rasa iko da birni mafi girma a kasar, wato Johannesburg karon farko tun bayan kawo karshen mulkin wariya.

Yanzu dai Herman Mashaba na jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance shi ne, magajin garin birnin na Johannesburg.

Tuni ya yi alkawarin aiwatar da gagarumin sauyi dangane da yadda ake gudanar da mulkin birnin wanda shi ne cibiyar kasuwancin kasar.

Jam'iyyar ANC dai ta fuskanci koma ba ya da ba a taba ganin irinsa ba cikin shekaru 20.

Yayin zaben larduna da aka yi cikin watan jiya ANC ta rasa iko da biranen Pretoria da kuma Port Elizabeth.

Labarai masu alaka