Kerry ya gana da Kenyyata a kan tsaro

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, yana tattaunawa da shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta a kan batun tsaro a yankin gabashin Afirka.

Ana sa ran ajandar tattaunawar za ta ƙunshi yaƙin da ake yi a Sudan ta Kudu da kuma halin da ake ciki a Somalia, inda masu tsattsauran ra'ayin Musulunci na Al-Shabab ke ci gaba da kaddamar da hare-hare.

Daga bisani Mista Kerry zai bi sahun ministocin harkokin waje na kasashe takwas na Gabashin Afirka don wata ganawa.

Zai kuma tafi Najeriya a ranar Talata domin tattaunawa a kan yaƙi da wata kungiyar ta masu tsattsauran ra'ayin Musulunci, Boko Haram.

Labarai masu alaka