Kerry zai fara ziyara a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption John Kerry

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry zai fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Najeriya.

Ana sa ran Mista Kerry zai gabatar da wani jawabi a birnin Sakkwato da ke arewacin ƙasar game da muhimmancin mutunta addinin juna wajen yaƙi da tsatsauran ra'ayi.

Sannan kuma zai tattauna da Shugaba Muhammadu Buhari, a kan matsalar tsaro da ta tattalin arzikin da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa.

Najeriya dai ta kwashe shekaru da dama tana fama da rikicin 'yan ƙungiyar Boko Haram, musamman a yankin arewa-maso-gabashin ƙasar.

Yayin kuma a baya-bayan nan ƙasar na fuskantar ta da ƙayar baya a yankin Niger-Delta mai arzikin mai.

Labarai masu alaka