Najeriya: Matakan gaggawa na farfado da tattalin arziki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption shugaban najeriya

A Najeriya wasu rahotanni na cewa, shugaban kasar Muhammadu Buhari zai nemi majalisar dokokin kasar ta ba shi wata dama ta musamman ta yadda zai iya aiwatar da wani shiri na gaggawa domin farfado da tattalin arzikin kasar.

Rahotannin dai na nuna cewa, shugaba Buharin yana neman hanyoyin da gwamnatinsa za ta gyara wasu dokoki ne, da za su kai ga hanzarta matakan farfado da tattalin arzikin kasar.

Sai dai a martanin da fadar shugaban ta mayar kan wannan magana ta ce, lamarin ba haka yake ba.

Kakakin shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya ce, shawarwari ne kawai wasu masana tattalin arziki suka gabatar wa gwamnati da suke ganin zasu taimaka wajen ceto tattalin arzikin Nigeria daga mawuyacin halin da ya shiga.

Faduwar farashin danyen mai ta kawo gagarumin koma bayan kudin shiga da gwamnatin Nigeria take samu.

Labarai masu alaka