Rio Olympics: Abubuwan da ba za a manta ba

Abu na farko da aka fara yi a birnin Rio da ba za a mance da shi ba a Olympic da aka yi a Brazil, shi ne kunna wutar da ke nuna bikin bude wasannin wanda Vanderlei de Lima, na Brazil ya yi.

Shi ne mutumin da ya ci wa ƙasar lambar tagulla a tseren fanfalaƙi a gasar Olympic na 2004.

Shi ya kamata ya lashe gasar, amma wani ɗan kallo ya shiga ya ture shi daga tseren, dalilin da ya sa ya zo na uku a tseren.

Gasar da aka yi a birninRio ita ce ta farko da aka samu tawagar 'yan gudun hijira su 10 da suka haɗa da guda biyar daga Sudan ta Kudu da biyu daga Syria da wasu biyun daga Jamhuriyar Congo da guda daya daga Habasha.

Lokacin da suke maci sun sha tafi a filin wasa na Maracana.

Wani hoto da ya nuna yadda wasannin Olympic ya hado mutane manya da ƙanana shi ne hoton da Ba'amurkiya, mai wasan alkafura, Ragan Smith ta ɗauka da DeAndre Jordan mai wasan kwallon kwando.

Tana sanya hoton ya ja hankali sosai a intanet.

Hakkin mallakar hoto bbc

Lee Goim yar wasan Korea ta Kudu ta ɗauki hoto da Hong Un Jong ta Korea ta Arewa, dukkansu masu wasan alkafura, abin da ke nuna 'yan uwantaka a tsakaninsu duk da takaddamar da ke tsakanin ƙasashensu.

Farin cikin Rafaela 'yar Brazil

Brazil ta fara lashe lambar zinare a wasan judo ajin nauyin kilo 57 na mata, kuma Rafaela Silva ce ta lashe.

'Yar wasan ta haskaka garin da ta fito mai fama da ƙuncin talauci a ƙasar ta Brazil wato City of God.

An hana Rafaela shiga wasanni a gasar Olympics da aka yi a Londan a shekarar 2012, saboda haka lashe lambar zinare da ta yi a wannan gasar ya nuna ƙwazonta wajen cimma burinta.

Michael Phelps ya yi murmushi bayan ya tserewa abokin hamayyarsa na Afrika ta Kudu, Chad Le Clos a wasan ninkaya na mita 200, mai salon malam bude mana littafi.

Sai dai wasu sun ce kamata ya yi Chad le Clos ya mayar da hankalinsa kan ninƙayar maimakon kallon abokin hamayyarsa.

Ɗan wasan ninƙaya ɗan gudun hijira

Ɗan ƙasar Syria, Rami Anis shi ne wanda ya wakilci tawagar 'yan gudun hijira a wasan ninkaya.

Rami ya gujewa yaƙin da ake yi a ƙasarsa a shekarar 2015, inda ya bi ta tekun Bahar Rum zuwa Turkiya.

Duk da dai bai samu lambar yabo ba a tseren mita 100, an yi ta masa tafi tun daga lokacin da ya fara tseren har zuwa lokacin da ya kammala.

'Yar Amurka, Simone Biles, mai shekara 19 ta mamaye wasan alkafura, inda ta dinga yin abin mamaki iri-iri a gasar, dalilin da ya sa ta ci lambar zinare hudu da azurfa ɗaya.

Bajintar da take yi a fili ya sa mutumin da ya yi tafiya a duniyar wata, Buzz Aldrin ya dinga kallonta.

'Yar wasan kwallon boli na yashi

Wani hoton da ya ja hankalin al'umma a kafar sada zumunta a duniya shi ne na 'yan wasan kwallo boli na mata, bayan da 'yar kasar Masar, Doaa Elghobashy, ta yi wasan sanye da kayan da ya rufe jikinta.

Ninƙayar mata ta mita 800

Katie Ledecky 'yar Amurka ta mamaye wasan ninƙaya, inda ta kafa tarihin lashe a kurme na mita 800 a cikin mintoci takwas da dakika hudu.

Hakan ya shafe tarihin da ta kafa a baya kuma ita ce ta lashe ninƙayar mita 200 da na 400 da kuma na 200 na 'yan wasa hudu.

Almaz ta Habasha ta lashe gudun mita 10,000

Almaz Ayana ce ta kafa tarihi na farko a filin wasan Olympic da aka yi a Rio, inda ta lashe lambar zinare a gudun mita 10,000.

Ɗan Ƙasar Masar El-Shehaby ya jawo cece-kuce bayan da ya Ƙi yin hannu da Or Sason na Isra'ila wanda ya doke shi a wasan judo ajin nauyin kilo 100.

Hakan ya sa 'yan kallo suka dinga yi masa ihu, daga baya aka mayar da shi gida.

Hoton Joseph Schooling na Singapore

Joseph Schooling mai shekara 13, wanda yake kwaikwayon Michael Phelps ya yi nasarar doke Phelps ɗin a ninƙayar mita 100.

Inda gwarzon nasa ya yi na biyu tare da dan Afirka ta Kudu, Chad Le Clos sai kuma Laszlo Cseh ya yi na uku.

Laurine van Riessen ta Netherlands da Virginie Cueff ta Faransa sun kusa yin karo a lokacin da suke tseren keke.

Hoton tseren nasu ya ja hankali a lokacin da Laurine ta kaucewa hadarin, wanda kadan ya rage ta fita daga filin wasa.

Ɗan tseren Birtaniya, Mo Farah ya faɗi a lokacin da yake tsaka da gudun kare kambunsa a gudun mita 10,000.

Amma nan da nan ya mike ya ci gaba da gudu har ta kai shi ga sake lashe gasar.

Neman aure

'Yar kasar China mai wasan ninƙaya na springboard ta ci lambar azurfa a wasan, sai saurayinta, Qin Kai ya durƙusa a gabanta a kan dandamalin da za a karramata ya mika mata zobe domin neman amincewar ta aure shi.

Nan take ta masa masa da na'am.

Hakkin mallakar hoto Getty

A lokacin da Usain Bolt ke tseren daf da ƙarshe ya samu damar da ya kalli kamara har ya yi mata murmushi. Daga baya ya kuma fafata ya lashe tseren mita 100 a mintoci 9.81, kuma karo na uku kenan da ya ci zinare a wasan Olympic uku.

Wayde van Niekerk

Ɗan Ƙasar Afirka ta Kudu, Wayde van Niekerk, ya kafa tarihin lashe tseren mita 400, bayan da ya shafe tarihin da Michael Johnson ya kafa shekaru 17 da suka wuce.

Nasarar da aka danganta da kakarsa mai shekara 74 wadda ta horar da shi.

Dan Birtaniya Nick Skelton, shi ne dattijon da ya lashe lambar zinare a wasan dawaki.

Sai dai dattijon mai shekara 58 ya ce ba zai shiga gasar Olympics da za a yi nan da shekaru huɗu ba a birnin Tokyo.

Usain Bolt

A wasannin na Olympic Usain Bolt ya ci zinare uku a tsere mita 100 da 200 da kuma na 100 na 'yan wasa hudu, hakan ya sa ya hada guda tara a gasa uku, kuma da wahala a samu wanda zai doke wannan tarihin a nan kusa.

Neymar da Brazil

A karon farko Brazil ta ci lambar zinare a fagen tamaula, kuma lambar da ba ta ci ba kenan a tarhin kwallon kafa.

Brazil ta buga 1-1 da Jamus, hakan ta kai su ga bugun fenariti, inda Brazil ta yi nasara.

Hakkin mallakar hoto AP

An yi bukukuwan rufe gasar tare da kashe wutar Olympics. Sannan firai ministan Japan, Shinzo Abe ya yi shiga irin ta tauraron wasan kwamfutan nan Super Mario. Japan ce dai zata ɗauki baƙuncin gasar ta Olympics nan da shekaru huɗu masu zuwa.

Labarai masu alaka