Wani ya amsa laifin rusa wuraren tarihi a Timbuktu

Hakkin mallakar hoto AP

Wani mai fafutukar Islama ɗan ƙasar Mali, ya amsa laifin tuhumar da aka yi masa ta rusa wuraren tarihi na Majalisar Dinkin Duniya a Timbuktu.

Ahmad al-Faqi al-Mahdi shi ne mutum na farko da ya taɓa fuskantar irin wannan tuhuma, a gaban kotun hukunta manyan laifukan yaƙi ta duniya, ICC.

Mutumin ya shaida wa kotun cewa ya yi nadamar jagorantar rusa wuraren, kuma yana fata babu wani Musulmi da zai yi koyi da abin da ya aikata.

Ana zargin ɗan fafutukar da rusa wureren bauta guda tara da kuma wani masallaci a Timbuktu a arewacin Mali a shekarar 2012.

Ahmad zai iya fuskantar ɗaurin shekara 30 a gidan yari.