Turkiyya za ta yanke hulɗa da Austria

Hakkin mallakar hoto EPA

Turkiyya zata janye jakadanta daga Austria.

Dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ta soma yin tsami ne cikin 'yan makonnin nan yayin da Austria ta yi kashedin cewa, Turkiyya tana kan hanyar aukawa cikin mulkin danniya.

Austria ta kuma yi kiran a sake duba batun tattaunawar shigar Turkiyya cikin kungiyar tarayyar Turai.

Wannan matsayi na Austria ya fusata Turkiyya inda ta ce, Austria ce, cibiyar nuna wariya a nahiyar Turai.

Labarai masu alaka