Birtaniya: Za a kebe fursunoni 'yan ta'adda

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An dauki wannan mataki ne bayan an samu Malam Anjam Choudary da laifin kokarin shigar da mutane kungiyar IS

Gwamnatin Birtaniya ta ce za a kirkiri wani sashi na musamman sabo da fursunoni masu tsattsauran ra'ayi a Ingila da Wales.

Ministar shari'a Liz Truss ta kuma bayyana wasu tsare tsare na cire duka litattafen da suke koyar da tsattsauran ra'ayi daga daukunan karatu a gidajen yari, da kuma kara tantance masu wa'azin addinai a gidanjen yarin.

To sai dai asusun garen-bawul kan gidajen yari sun yi gargadin cewa gidajen yarin suna fama da karancin ma'aikata.

Wannan mataki dai na zuwa ne bayan wani rahoto ya gano cewa ana samun matsalar karuwar masu zazzafan kishin addini a gidajen yari.

Tace babu yadda za a yi a kyale wasu daurarru su ringa gurbata tunanin takwarorin su a gidajen kaso.

Dan haka a yanzu za a kafa wasu kananan dakuna na musamman domin ajiye fursunoni masu tsatssauran ra'ayi.

An dauki wannan mataki ne bayan an samu Malam Anjam Choudary da laifin kokarin shigar da mutane kungiyar IS a lokacin da ya ke tsare a gidan kaso.

To sai dai wasu masu ruwa da tsaki a harkar gidajen yari na ganin cewa wannan tsari zai yi tasiri ne kawai idan ana ajiye mutane a wajen na dan wani lokaci, amma ba dun-dun-dun ba.