'Mutane 65,000 na fuskantar yunwa a Borno da Yobe'

Hakkin mallakar hoto AFP

Majalisar ɗinkin duniya ta ce yawan masu matuƙar buƙatar tallafin abinci a yankin arewa-maso-gabas na Najeriya ya rubanya.

Alƙaluman hukumar samar da abinci ta majalisar ta fitar sun nuna cewa, aƙalla mutane 65,000 da ke zaune a yankunan da aka ƙwato daga 'yan Boko Haram lamarin ya shafa.

Inda ta bayyana cewa mutanen suna fuskantar yanayi da ya yi kama da na bala'in yunwa mai tsanani.

Sanarwar da jami'in hukumar mai kula da yammacin Afirka, Abdou Dieng, ya fitar ta ce a jihohin Borno da Yobe yawan mutanen da ke fama da rashin abinci yana ƙaruwa sosai.

A cewarta daga watan Maris da ya gabata zuwa tsakiyar watan Agusta yawan mutanen ya nunka zuwa fiye da kashi hudu.

Hukumar ta kuma ce rikicin Boko Haram da ya raba dubban mutane da muhallansu da sana'oinsu ya jefa su cikin matsalar matuƙar ƙarancin abinci.

Yayin da ta ce tana buƙatar aƙalla dalar Amurka miliyan 52 domin ci gaba da samar da tallafin abinci na gaggawa a arewa-maso-gabashin Najeriya.