Nougat: Sabuwar manhajar Google

Hakkin mallakar hoto

Kanfanin fasaha na Google ya fito da sabuwar manhajar wayar komai-da-ruwanka ta Android 7.0. An kuma yi wa sabuwar manhajar lakabi da suna Nougat.

Ita dai wannan sabuwar manhaja ta wayar salula tana dauke da sabbin karin abubuwa wadanda manhajojin da kamfanin ya yi a baya ba sa dauke da su.

Ta na amfani da shafuka ko Apps biyu a lokaci daya, tare kuma da bada damar amfani da hotunan bidiyo masu nauyi ko sarkakiya cikin sauki ba tare da wata tangarda ba.

To sai dai kuma ba dukkanin sanfuran wayoyi ba ne za su iya amfani da wannan sabuwar manhaja ta Google ta Android 7.0.

Ana sa ran kamfanonin waya za su yi kokarin inganta wayoyin nasu yadda za su iya amfani da manhajar nan da wani dan lokaci.

Labarai masu alaka