Sai da goyon bayan jama'a za a kawar da BH - Kerry

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya ce Nigeria ba za ta iya kawar da kungiyar Boko Haram ba har sai al'ummar kasar sun yi cikakkiyar amincewa da gwamnati da kuma sojojin kasar.

A jawabin da ya yi a fadar Sarkin Musulmi a Sokoto, Mista Kerry ya ce "samun nasara kan Boko Haram a fagen daga abu ne da ya zama wajibi mu yi".

Ya ce hakan na bukatar hadin kan jama'a, wanda ba zai samu ba sai da goyon bayan soji da sauran hukumomin tsaro.

"Ba a samun nasara kan tsattsauran ra'ayi ta hanyar amfani da bingida ko tsorataswa," in ji Mista Kerry.

Ga karin jawabin da Mista Kerry ya yi a kan wasu batutuwan:

Ilimin Mata

John Kerry ya ce bai wa mata ilimi yana da matukar muhimmanci kuma buri ne da shugaba Muhammadu buhari yake da shi domin tabbatar da ci gaba a rayuwar mata da kuma ci gaban al'umma.

Sakataren wajen na Amurka ya kara da cewa, ya ya yi farin ciki kwarai game da shirin da Mai girma sarkin Musulmi, Muhammadu sa'ad Abubakar ya kaddamar na zuba jari a karatun mata da kuma makarantar kiwon lafiya ta mata da ya bude.

"Idan aka ilimantar da mata kuma aka karfafa musu gwiwa, an fi samun ci gaba a al'umma kuma an fi morar rayuwa".

Cin hanci

Sakataren harkokin wajen Amurkar ya kuma yi jawabi a kan cin hanci, inda ya jaddada cewa dole ne shugabannin kasashen duniya su hada kai domin yaki da cin hanci ta yadda za a samu kyakkyawan shugabanci mai dorewa.

"Cin hanci, ba wai laifi da abin kunya ba ne kawai, yana da hadari" a cewar Mista Kerry.

Hakazalika ya bayyana cewa kasashen duniya na asarar dala tiriliyan 2.6 na tattalin arzikinsu a sanadiyar cin hanci.

Tsattsauran ra'ayi

A jawabin nasa, ya yi bayani a kan tsattsauran ra'ayi inda ya yaba da irin kokarin da shugaba Muhammadu Buhari ya ke yi na kawar da kungiyar Boko Haram da ta addabi kasar.

Hakkin mallakar hoto AP

Mista Kerry ya ce "Samun nasara kan Boko Haram a fagen daga abu ne da ya zama wajibi". Ya ce hakan na bukatar hadin kan jama'a, wanda ba zai samu ba sai da goyon bayan soji da sauran hukumomin tsaron kasar.

Akalla mutane 20,000 ne aka kashe a shekaru bakwai da aka shafe ana rikicin Boko Haram, sannan fiye da miliyan biyu suka rasa muhallansu.

Nan gaba a ranar Talata ne ake sa ran Mista Kerry zai gana Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a kan matsalar tsaro da tattalin arzikin da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa.

Labarai masu alaka