An tsare mutumin da ya sa wa karensa Buhari a Kurkuku

Hakkin mallakar hoto Eshna Benegal

Wata kotun majistare da ke a Sango Ota a jihar Ogun ta umarci a ci gaba da tsare Joe Chinakwe, mutumin nan da ya sanyawa karensa suna Buhari.

Rundunar 'yan sandan jihar ce dai ta gurfanar da Joe Fortomose Chinakwe a gaban kotun majistare, bisa zargin shirin tada zaune tsaye, sakamakon yawon da yake yi da karensa, wanda ya rubuta sunan Buhari a sassan jikin karen.

Kotun dai ta bada belinsa, to sai dai bai cika sharudan beli ba, dan haka aka ci gaba da tsare shi a gidan kaso.

Tun da farko dai shugabannin kananan kabilun dake zaune a jihar ta Ogun sun shiga tsakani da niyyar kawo karshen tuhumar da ake yiwa mutumin.

To sai dai rundunar 'yan sandan jihar ta sake gayyatar sa inda ta gurfanar da shi a kotu.

A yanzu dai sarkin Hausawa na jihar ta Ogun ya sheda wa BBC cewa za su sake wani yunkurin na karbar belin Joe Fortomose Chinakwe da kuma nufin janye tuhumar da ake yi masa, a wani mataki na sasanta batun.

Ranar 19 ga watan gobe ne dai za a ci gaba da shari'ar mutumin.

Labarai masu alaka