Niger na fuskantar matsin tattalin arziki

Hakkin mallakar hoto

A jamhuriyar Nijar, mutane da dama musamman 'yan kasuwa na fuskantar matsin tattalin arziki.

Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum, da wasu 'yan kasuwa na kasar sun ci gaba da yin tsokaci game da matsin da ake cewa tattalin arzikin kasar ya fada a ciki.

'Yan kasuwa na kokawa da rashin samun ciniki saboda rashin jujjuyawar kudade a hannun jama'a.

Wasu 'yan kasar da dama dai na ganin hakan ya samo asali ne daga matakan da gwamnatin kasar ta dauka wajen yaki da almundahana.

Labarai masu alaka