'Hari ta sama ya jikkita Shekau' -inji Sojoji

Hakkin mallakar hoto AFP

A Najeriya sojojin kasar sun ce, wani hari da dakarun sama suka kai ya kashe wasu jiga-jigai a ƙungiyar Boko Haram.

Wata sanarwa da kakakin sojan ƙasa, Kanar Sani Kukasheka Usman ya fitar ta ce, yayin hare-hare ta sama da aka kai ranar Juma'ar da ta gabata an kuma jikkata daya daga cikin shugabannin Boko Haram, wato Abubakar Shekau.

Daga cikin manyan 'yan kungiyar ta Boko Haram da aka kashe yayin harin sun haɗa da Abubakar Mubi, da Malam Nuhu da Malam Hamman.

Sanarwar ta kuma ce, an kai harin ne a ƙauyen Taye dake yankin Gombale, dake dajin Sambisa.

Kungiyar Boko Haram ta shafe shekaru tana fafatawa da sojojin Najeriya a yankin arewa maso gabashin kasar.

Sai dai kuma wannan ba shi ne karon farko ba da sojojin Nigeria suke ikirarin kashe wasu shugabannin Boko Haram.