Sudan ta bawa Riek Marchar masauki

Hakkin mallakar hoto AFP

Gwamnatin Sudan ta ce ta bawa tsohon mataimakin shugaban Sudan ta kudu Riek Machar masauki.

A watan jiya ne dai shugaban Sudan ta kudu Salva kiir ya sauke Machar daga mukamin sa, bayan da suka jima suna takun saka.

Kakakin gwamnatin Sudan Ahmad Bilal ya ce an amince a karbi Riek sabo da dalilai na jin kai, kuma an bashi kulawar lafiya ta gaggawa.

Yace yanzu haka Machar ya na cikin kyakkyawan yanayi, sai dai bai bayyana irin larurar da ya ke fama da ita ba.

A makon jiya ne dai aka bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban ya bar Sudan ta kudu bayan sauke shi da aka yi a watan Yuli, a lokacin da ake tsananin fafatwa tsakanin sojojin gwamnati da na Riek Machar a Juba, babban birnin kasar.

Labarai masu alaka