Turkiya ta umarci mazauna Karkamis su fice

Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumomin Tukiya sun umarci mutanen dake zaune a garin Karkamis a arewacin kasar su fice daga gidajen su, bayan wani hari da kungiyar IS ta kai yankin.

Kungiyar ta IS mai da'awar kafa daular musulunci ta kai harin ne kan garin dake kan iyaka daga garin Jarablus da ke kan iyakar Syria da Turkiya.

A yanzu haka dai sojoji 'yan tawaye da ke samun goyon baya daga Turkiya na shirin kwace garin.

Turkiya dai ta zargi kungiyar IS da kai harin kunar bakin wake wanda ya janyo mutuwar mutane da dama a kudancin kasar a karshen makon jiya.

Dan haka a cewar ta wajibi ne a kawar da IS din daga garin, wanda yake kan iyaka.

Labarai masu alaka