Afghanistan: An kai hari a jami'a

Hakkin mallakar hoto AP

Jami'an tsaron Afghanistan suna ci gaba da neman 'yan bindiga biyu da suka kai hari a harabar jami'ar American University mai zaman kanta a birnin Kabul.

'Yan bindigar sun kai harin ne da maraicen Laraba, inda aka ji ƙara mai ƙarfin gaske, sai kuma harbi ba ƙaƙƙautawa ya biyo baya.

Lamarin yasa dalibai sun yi ƙoƙarin tsira ta kowacce hanya.

Ya zuwa yanzu dai babu tabbas akan adadin wadanda lamarin ya shafa.

Amma rahotanni sun ce, an kashe wani maigadi, kuma dalibai da dama sun jikkata.

Har yanzu ba a san ko ta yaya 'yan bindigar suka auka cikin jami'ar ba.

Labarai masu alaka