An kama masu amfani da WhatsApp a Burundi

'Yan sanda a Burundi suna ci gaba da tsare mutane tawkas da ake zargin da bata sunan gwamnati a dandalin sada zumunta na WhatsApp.

An cafke wadanda ake zargin ne a lokacin da suke wata ganawa wanda 'yan sanda suka ce ta kitsa yadda za su kara yada labaran karya ne.

Tun a bara ne dai aka fara samun rudani a kasar ta Burundi, lokacin da mummunan tashin hankali ya barke saboda neman sake tsawaya takara a karo na uku da shugaba Pierre Nkurunziza ya yi.

Masu sukar gwamnatin Burundi sun ce cafke mutanen takwas wani mataki ne na takaita 'yancin yada bayanai a kasar.

Amma kuma mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ya zargi 'yan kungiyar ta Whatsapp da haddasa mummunan tashin hankali bara a kasar.

Ya ce za a dauki tsauraran matakai kan mutanen da ke yada jita-jita a shafukan sada zumunta.

Shafukan sada zumunta sun kasance wasu hanyoyin da suka fi yin fice wajen samun labarai, bayan da aka rufe gidajen rediyo da dama a bara a kasar.

Labarai masu alaka