Coci na tallafa wa 'yan gudun hijirar Boko Haram

Rikicin Boko Haram da ya addabi yankin tafkin chadi da arewa-maso-gabashin Najeriya, ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 20,000 yayin da sama da mutane miliyan biyu kuma suka rasa muhallansu.

A sanadiyyar rikicin na Boko Haram a arewa-maso-gabashin Najeriya, a halin yanzu yara marayu 3,000 ne da kuma wasu mata 30 da mazanjensu suka mutu suka tsinci kansu a wani sansanin 'yan gudun hijira da ake kira "gidan mabukata".

'Yan gudun hijirar sun shafe shekaru biyu zuwa hudu suna sansanin da ke karkashin jagorancin cibiyar ayyukan kiristoci na duniya ta ICCM, da ke yankin Uhogua a wajen birnin Benin na jihar Edo da ke yankin Niger Delta a Najeriya.

Akwai walwala a sansanin sakamakon sojoji da 'yan sanda da kuma wasu jami'an tsaron jihar da ke tsaron kofar shiga.

Kuma wakilin BBC ya samu wasu yara suna wasan kwallon kafa, wasu kuma suna lilo da ma dai sauransu.

Akwai yara sama da 2500 da kuma mata 30 wadanda mazajensu suka mutu a sansanin, wadanda suka yi gudun hijira daga jihohin Borno da Adamawa a cewar Fasto Evelyn Omigie, shugaban sansanin.

"A lokacin da yaran suka zo nan, suna cikin wani mawuyacin hali, suna fama da tamowa da rashin isasshiyar lafiya. Hakan ya faru ne sakamakon wahalar da suka fuskanta;, wani yaron ma ya shafe wata uku a cikin kogo babu abinci mai kyau sai ciyawa yake ci.

Amma mun basu kulawa kuma musamman abin da ya shafi tunaninsu kuma yanzu ka ga duk sun rabu da raunin da suke fama da shi kuma yanzu suna wasansu".

A hankali, yaran suna manatawa da tashin hankalin da suka fuskanta a baya a cewar daya daga cikinsu, Johanna Yohanna".

"Shekarata 16 na gudo wannan sansanin a shekarar da ta gabata daga garin Goshe da ke karamar hukamar goza a jihar Borno saboda rikicin Boko Haram. Mahaifi na ya mutu kuma ban san inda mahaifiyata ta ke ba."

Philemon Obadiah mai shekaru 17, bai san inda iyayensa suke ba, "Bana jin dadi saboda kusan shekara ta uku yanzu ban ga iyaye na ba kuma kila suma suna tunani na don haka ne bana jin dadi. Ina fatan mu koma garinmu nan ba da dadewa ba."

Matan da mazansu suka mutu wadanda ke zaune a sansanin suma suna kokarin farfadowa daga iftila'in da suka fuskanta a baya.

Tani Philemon, mai shekara 38 wadda mijinta ya mutu ta ce yanzu tafi jin dadi, "Mun gode wa Allah da irin rayuwar da muke yi a wannan sansanin, ana bamu kyakkyawar kulawa musaman a bangaren abinci da tufafi da wasu bukatun namu na yau da kullum. Ana kuma bamu horo a kan yadda ake yin sabulu da dinki da sauran sana'oin hannu."

Suna na Nancy Joseph "Yan kungiyar boko Haram sun shiga garinmu da misalin karfe 11 da dare suka kore mu. Sun kashe mijina a gaba na suka bar ni da yara tara. Shi yasa na gudo na zo wannan sansanin.

Joseph David, ya yi wa BBC bayanin yadda ya zama maraya, " 'Yan Boko Haram sun kai hari kauyenmu, Gwoza sau 12, saboda haka ne na shafe kwana uku ina tafiya a kasa, babu abinci babu ruwan sha har sai da na kai garin Madagali da ke jihar Adamawa. Daga baya kuma sai suka kai hari a wurin da iyaye na suka buya, sun kashe mahaifi na, sun gurbata ruwan da mahaifiyata ta sha kuma a nan ta ke ta mutu."

Gidauniyar We Care Trust Foundation ta matar gwamnan Jihar Edo, Mis Lara Oshiomole ta ce ana bai wa 'yan gudun hijirar horo a bangarorin kamun kifi da noman kayan lambu da noman kayan abinci da yadda ake adana su da dinki da kuma horo a kan hanyoyin sadarwa na zamani.

Ta ce "Ana fama wajen bai wa yaran kulawa, mutane na kokari domin ganin cewa yaran na cikin walwala da farin ciki kuma mun yi sa'a sosai da mu ke samun tallafi daga wurare daban-daban na kasar. Muna musu godiya".

Ana zargin cewa wasu daga cikin 'yan gudun hijirar musulumai ne a lokacin da suka iso sansanin, amma daga baya sai suka sauya zuwa kiristoci.

Sai dai wasu daga cikin yaran da suka zanta da BBC sun munsanta zargin, inda suka ce "Dama can mu kiristoci ne kafin muzo wannan sansanin, mu haifafun kiritoci ne, hasali ma, iyayenmu ma kiristoci ne. Don haka babu musulumi ko daya a cikinmu".

Shugaban sansanin, Fasto Solomon Folorunsho ya kara da cewa, "Muna aiki tare da 'yan sanda da rundunar tsaron farin kaya da hukumar tsaron farin kaya ta jiha da wasu hukumomin tsaro na kasa da kuma hukumar tsaro ta jihar Edo".

Ciyar da 'yan gudun hijirar aiki ne mai wahala sosai, saboda ana dafa buhuhunan shinkafa 13 a duk lokacin cin abinci, saboda haka ana bukatar tallafi sosai a bangaren abinci da wasu kayan amfani a sansanin, a cewar Fasto Evelyn Omigie, daya daga cikin shugabannin sansanin 'yan gudun hijrar.

Ya zuwa yanzu da taimakon kungiyar agaji ta Red Cross da ma'aikatar kula da harkokin mata da hukumar tsaro ta jihar da sauran hukumomin da ke aiki da sansanin, an gano iyayen wasu daga cikin yaran a Kamaru da wasu wuraren kuma an hada su da yaransu.