Hajj: Za a samar da tantuna masu rage zafin rana

Hakkin mallakar hoto AP

Mahajjatan bana 82,000 zasu amfana da tantuna masu rage zafin rana da aka samar a filin Arfa.

Mahajjata daga ƙasashen Turkiyya, Turai da Amurka da Australia ne zasu amfana da waɗannan hemomi da za a samar.

Jaridar Saudi Gazette ta ce, jagoran kamfanin hidimar alhazan da ya samar da tantunan, Tariq Anqawi ya ce, an ɗau wannan mataki ne domin ana sa ran fuskantar zafin rana mai tsanani yayin aikin hajjin bana.

Wannan dai wani mataki ne da kamfanin ya dauka domin kara kyautatawa alhazan da yake yi wa hidima bana.

Labarai masu alaka