Girgizar ƙasa ta kashe mutane 38 a Italiya

Image caption Ana fargabar mutanen da suka mutu za su iya karuwa

Aƙalla mutane 38 ne wata girgizar ƙasa mai ƙarfi ta kashe a tsakiyar Italiya tare da lalata ƙauyuka da kuma garuruwa da dama.

Girgizar ƙasar mai ƙarfin maki shida da digo biyu ta lalata gine-gine a wurare da dama, yayin da ake neman mutane 150.

Magajin garin Amatrice ya ce ana jin muryar mutane daga ƙarƙashin baraguzai, yayin da ake ci gaba da ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Lardunan da lamarin ya shafa, Umbria da Lazio da Marche wurare ne da masu yawaon buɗe idanu ke zama.

Labarai masu alaka