Daliban Kano a waje sun shiga tsaka mai wuya

Image caption Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje

Daliban Kano da gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyin karatunsu a kasashen waje na fama da mawuyacin halin da suka shiga, sakamakon rashin biyan su kudin abinci da na wurin zama na watanni.

Wasu daliban sun ce lamarin na barazana ga karatun nasu don kuwa jami'o'insu sun ce sai sun cika kudin makarantar da ake bin su kafin su ci gaba da daukar darasi.

Daya daga dalibai 40 'yan asalin jihar ta Kano da ke karatu a jami'ar October Six ta Masar ya ce tsawon wata 10 ke nan ba a ba su kudin abinci ba, kuma tun a bara bizarsu ta kare, al'amarin da ya sa suke wasan buya a jami'ar.

Khalid Mahmud, shi ma wani mai karatu ne a India kuma jagoran daliban jihar Kano da ke karatu a ketare ya ce "wasu dalibaina sun shafe wata 13 ba a biya su kudin abinci ba."

Ya kuma kara da cewa daliban Sudan 103 su ma sun kwashe wata 10 ba kudin abinci da kudin wurin kwana, har ta kai an kori wasu daga gidajen da suke haya.

Akwai kuma wasu daliban jihar ta Kano 181 da suka je Uganda don karatun fasahar sadarwa, wadanda sun kasa komawa gida, bayan kammala karatunsu.

Sai dai kuma wasu daga cikinsu sun samu dawowa gida amma sun ba su karbi takardun shaidar kammala karatun ba saboda gwamnati ta gaza biyan cikon kudin makarantarsu.

To sai dai Babbar sakatariya a hukumar tallafin karatu ta Kano, Farfesa Fatima Mohammed Umar ta shaida wa BBC cewa al'amarin ba haka yake ba.

Ta ce sabanin ikirarin cewa suna bin bashin kudin abinci na sama da wata 10, daliban na bin bashin kudin wata biyar ne kawai, bayan kudin wata uku da gwamnati ke ci gaba da biya a yanzu.

Ta kara da cewa game da cikon kudin makarantu da na wurin zama da daliban ke bin bashi, majalisar zartarwar jihar Kano, ta amince da biyan wadannan kudi.

Kkuma yanzu haka batun yana gaban ma'aikatar kudi, sai dai, babbar sakatariyar ba ta ba da tabbacin ranar fitar kudin ba.