Sojin Turkiyya sun kutsa kai Syria

Sojin Turkiyya Hakkin mallakar hoto AFP

Motocin yaki na kasar Turkiyya sun nausa zuwa cikin kasar Syria domin korar mayakan kungiyar masu ikirarin kafa daular Musulunci ta IS daga yankunan iyakar kasarta.

Gabannin hakan an yi ɓarin wuta a kan wuraren da ke hannun 'ya'yan ƙungiyar.

Wasu majiyoyin sojin Turkiyyar sun shaida wa kafafen yaɗa labarai na ƙasar cewa, harin ya lalata wurare 70 a Jarablus, yayin da wani harin ta sama ya lalata wasu wuraren 12.

'Yan tawayen Syria da ke samun goyon bayan Turkiyya na rufawa dakarun kasar baya a harin.

Turkiyya ta ce kutsen da ta yi cikin Syria ba kawai tana harin 'yan IS ba ne, har ma da mayakan Kurdawa da ke dauke da makamai.

Labarai masu alaka