India: Za a haramta wa mata daukar cikin wata

Hakkin mallakar hoto AP

Gwamnatin Indiya ta fito da wani kudurin dokar da zai haramta wa matan kasar sana'ar daukar cikin wasu mata.

Idan majalisa ta amince da dokar, za ta haramta wa matan kasar daukar ci ga mutane da ba 'yan kasa ba da matan da matan da basu da aure da kuma masu neman jinsi daya.

Sai dai a karkashin sabuwar dokar ma'auratan da basa iya haihuwa za su iya neman wata mace a cikin dangi ta daukar musu ciki.

Kungiyoyin da ke kula da rashin samun haihuwa sun soki shirin dokar, inda suka ce zai iya haifar da samun wuraren da ba a yarda dasu ba a hukunce da mata za su dinga samun juna biyun.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu sukar wannan kasuwancin, sun ce talauci ne ya ke sa mata da dama daukar irin wannan cikin

Ana kiran Indiya "cibiyar da mace ke daukar cikin wata macen" na duniya, inda ma'aurata a indiya, wadanda ba su iya haihuwa, har ma mutane da dama daga kasashen waje, ke zuwa su biyan mata kudi domin su yi musu renon dan tayi har haihuwa.

An kiyasta cewa a shekara wuraren samar da juna biyun na samar da fiye da dala biliyan daya a shekara.

Sai dai an nuna damuwa sosai a kan rashin doka a kan irin wannan hanyar kasuwancin.

Ministan harkokin wajen kasar, Sushma Swaraj, ya shaida wa manema labarai cewa, karkashin dokar da ake shirin samarwa ma'aurata yan kasar Indiya, wadanda suka shafe akalla shekara 5 da aure za su samu damar neman samun ciki, amma dole sai dai ta hanyar wata mace daga cikin daginsu.

Sushma ta shaida kuma bayyana cewa "Wannan kuduri ne wanda ya kunshi komai da komai wanda zai hana irin wannan kasuwancin."

"Ma'aurata marasa 'ya'ya wadanda likitoci suka bayyana musu cewar ba za su iya haihuwa ba, za su iya neman wata mace a cikin dangi ta taimaka musu.

Mutane da dama a kasar sun soki manufar, suna masu cewa za a sa ma'aurata wadanda suka zaku su haihu su zama basu da wani zabi.

"Duk da cewar muna bukatar dokar da zata tabbatar da cewar ba a tirsasawa mata daukar ciki ta wannan hanyar ba, hana daukar cikin ta wannan hanyar cikin gaggawa ba ayi tunani ba."

Kasar Indiya na da mutane marasa galihu daya bisa uku na duniya.

Masu suka sun yi amanna cewa talauci ne babban dalilin da ke sa mata ke daukarwa wasu matan ciki domin su samu kudi.

Labarai masu alaka