Sojin Amurka sun gargadi Iran

Hakkin mallakar hoto IRINN VIA AP

Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce daya daga cikin jiragen ruwan yakinta ya yi harbi irin na tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, bayan wani jirgin saman Iran na yaki ya tunkari inda jiragen ruwan Amurka na yaki suke girke a yankin tekun Fasha.

Kakakin Pentagon Peter Cook ya ce jirgin Iran din ya kusanci jiragen ruwan Amurka na yaki a lokuta da dama a cikin wannan makon, kuma hakan ba daidai ba ne, kuma wannan ne ya jirgin ruwan ya yi harbi irin na gargadi:

Ya ce ana daukar irin wadannan matakan ne domin Mu tabbbatar cewa Sojojinmu da kuma jiragen yakinmu sun kare kansu, tare da tabbatar da cewa lamarin bai yi muni ba.

Ya kara da cewa Amurka ba za ta yarda da wannan dabi'a ta Iran ba, tunda jiragen ruwan nata suna wani wuri da ke karkashin kasa da kasa.

Sai dai Ministan tsaron Janar Hosein Deh-ghan ya ce Iran za ta ci gaba da yin wannan sintirin don kalubalantar jiragen ruwan da suka yi mata kutse cikin kasarta

Labarai masu alaka