Girgizar ƙasa ta kashe mutane 247 a Italiya

Hakkin mallakar hoto AP

Yawan mutanen da girgizar ƙasa ta hallaka a yankin tsakiyar Italiya sun kai aƙalla 247.

Girgizar ƙasar da aka yi a ranar Laraba ta shafe garuruwa uku, inda babu abin da ya rage illa baraguzan gine-gine.

Masu aikin ceto a yankin tsakiyar Italiya sun kwashe dare suna amfani da diga, wani lokaci ma da hannayensu a kokarin zaƙulo wadanda suka makale a cikin baraguzan gine-gine.

Kakakin kungiyar agaji ta Red Cross, Tommaso Della Longa, ya ce irin barnar da girgizar kasar ta yi ba zata misaltu ba.

Kuma ya ce, yawancin wuraren da lamarin ya shafa sun yi kaca-kaca, ba abin da ya yi saura.

Labarai masu alaka