Turkiyya ta kare kutsen da ta yi a Syria

Hakkin mallakar hoto Getty

Turkiyya ta yi gargadin cewa tana da 'yancin ta kai dauki, muddin mayakan Kurdawa da ke Syria ba su yi abin da take bukata ba, na su janye zuwa gabashin kogin Euphrates a cikin mako guda.

Ministan tsaron Turkiyyan, Fikri Isik, ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da rahotanni ke nuna cewa wasu karin motocin yakin kasar sun sake ketara bakin iyaka zuwa arewacin Syria.

A ranar Laraba ne Turkiyyar ta fara kaddamar da kutsen a cikin Syria,matakin da ke samun goyon bayan Amurka.

Wani kawancen mayakan Kurdawa da aka sani da SDF ya kori mayakan IS daga garin Manbij, da ke yammacin Kogin Euphrates.

Kurdawa masu dauke da makamai na Syria, YPG, sun bayar da sanarwar cewa mayakansu sun janye daga Manbij zuwa sansanoninsu.

Labarai masu alaka